A tuntube mu a 08061654483

Name

Email *

Message *

Saturday, 21 April 2018

Yadda ake bude gmail Account

Sau da yawa mutane kan so su yi wani abu a saman internet, kamar buder account na website, da dai sauransu, amma rashin e-mail sai ka ga yana hana su yin wannan abu. Akwai da dama daga cikin mutance da ke turo mana da koken cewa su sun kasa bude e-mail account duk da kuma cewa sun yi iya bakin kokarinsu.

A cikin wannan kasida tamu ta yau, zama nuna muku hanyar da zaku bi a saukake domin bude e-mail (gmail). Amma ya kamata ka sani cewa, yafi matukar sauki sosai ka bude gmail da computer a maimakon yin amfani da waya. Zaka iya zuwa a kowace Café, minti goma ya ishe ka. Amma idan har baka iya samun damar yin amfani da computer, zaka iya amfani da waya (musamman ma android).

Ga wadannan matakai kamar haka:

Ka shiga website din gmail.com
Sai ka shiga wajen create new account
Wannan zaya kai ka zuwa inda zaka shigar da bayananka. Sai ka shigar da su kamar haka:

Bayan ka gama sai ka danna “Next Step”. Daga nan wani shafi zaya fito wanda zaya bukaci ka amince da sharudan google:

Daga nan zaka wuce  zuwa inda za’a bukaci kayi verifying din lambar wayarka. Sai ka zabi hanyar da kafi bukata, ko ta kira ko kuma ta message.

Idan ka sun baka code din (ta hanyar kira ko kuma ta hanyar message) Sai ka sanya a cikin wajen da zasu samar maka da shi (Kamar yadda zaka iya gani a cikin foton):
Da zaran kayi verirying ko kuma tabbatar da lambar wayarka zasu nuna wannan page da ke nuna cewa ka kammala komai.


Amma idan da waya zaka yi amfani, to tun a farko zaka fara sanya lambarka  ne sai su turo maka da wani link ta message. Wannan link din shine matayin verification code da zasu turo maka(idan kayi amfani da computer). Wannan link shi zaka bi domin ci gaba da rajistar.

Wadanan sune matakan da kake bukatar domin bude gmail accoount da kanka ba tare da ka baiwa wani kudi ba domin ya yi maka.