A tuntube mu a 08061654483

Name

Email *

Message *

Sunday, 23 February 2020

Wani Dan Arewa ya tsinci Dubu 200,000 ya maidawa Mai shi abun sa.

Wani Matashi Dan Arewa , Mai sana'ar wankin takalmi ya tsinci kudi , kimanin Dubu dari biyu a jahar Lagos .
Inda matashin ya maidawa Mai kudin kayan sa.
Wannan yasa Mai kudin ya bashi tukuicin dubu biyar ,Amma yaki karba , har sai da ya lallashe shi ,sannan ya karba.

Thursday, 23 May 2019

An zabi Tambuwal A matsayin Mataimakin Shugaban Gwamnonin Nigeria

Gwamnan jahar sokoto His Ex. Aminu Waziri Tambuwal ,ya Zama Mataimakin shugaban kungiyar Gwamnonin Nigeria .
A jiya Laraba 22-05-2019.
A yayin da kayode ya Zama Shugaban Gwamnonin Nigeria.

Thursday, 10 May 2018

AN KAMA YAN TA, ADDA A KADUNA.

LABARI MAI DADI
An Kama 'Yan Ta'adda Sama Da 50 Da Suka Addabi Yankin Birnin Gwari
Rundunar 'yan sanda Nijeriya ta gabatar mutune 56 barayin shanu da ake zargi da ta'ddanci da kuma kashe-kashen mutane hadi da garkuwa, fashi da makami da muggan makamai dake faruwa a yankin Birnin Gwari dake jihar Kaduna, da wasu kauyuka dake jihar Zamfara.

Friday, 4 May 2018

Ma'aurata sun tona wa kansu asiri gaban kotu a jihar Oyo, leka kuji

- Wasu ma'aurata da ke zaune a garin Ibadan sun yiwa junansu tonon silili a gaban Alkali

- Mijin ya roki kotu ta raba aurensu saboda tsabar sata da yace matar nasa ke yi masa

- Matar nasa tace ita ba barauniya bane amma ta kwashe wasu kayansa ta sayar ne saboda ya dena kula da ita

Wata kotu da ke zamanta a Mapo da ke Ibadan a jihar Oyo ta raba auren wani Akeem Folorunsho da Fatima saboda sata da yayi ikirarin matar na yi masa. Ma'auratan dai sun shafe shekaru biyu suna tare kuma Allah ya albarci auren da 'da daya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Alkalin kotun Cif Ademola Odunade ya amince da bukatar Akeem inda ya raba auren.

NEMAN TAIMAKO

NEMAN TAIMAKO
TAUSAYI DA AL'AJABI: An Haife Ta Da Kai Biyu Kuma Ana So A Cire Daya Ta Rayu
Wannan yarinyar da Kuke Gani daga Karamar Hukumar Garkon Jihar Kano Take. An Haife ta Da Wannan Larura ne A Goshinta Wanda Ta Kusa Girman Kanta Na Asali. Wanda Kullum Cutar Kara Girma Take Kamar Yadda Kuke Gani.
Yanzu Haka Dai Cutar Ta Fara Hana ta Bacci da Alama Tana Saka Mata Ciwon Kai Mai Tsanani. Likitoci Dai Na Ganin Wannan Cuta Za ta Iya Lalata Mata Kwakwalwa Matukar Ba a yi Maganin Abinda Wuri ba, wato Idan Ba'ayi Mata Aiki ba..
Yanzu Haka Iyayen Wannan Yarinya basu Da Abinda Za su Kai Wannan Yarinya Asibiti Da Za'ayi Mata Aikin. Haka Zalika Yanzu Suna Neman Naira Dubu Hamisin N50,000 Ne kafin Su Kai ta Asibitin Malam Aminu Kano Domin Ceto Rayuwarta.
Ga mai Bukatar Taimaka Mata Za ku Iya Amfani Da Wannan Lambar Account
Acc No 0178838804
Acc Auwal Abubakar kabir
GTbank
Domin Karin Bayani Kuna Iya Tuntubar Wannan Lamba Kamar Haka...08051192528